Latest Articles

Read All

  • Littafin Ƙabli da Ba’adi

    Littafin Ƙabli da Ba’adi • Rubutawa:    Aliyu M. Ahmad Sauƙe a PDF format ta  👉 DOWNLOAD •👉 Telegram   •👉 Whatsapp  • Blogs:       aliyumahmad.blogspot.com       aliyumahmad.art.blog • Nauyi (Size): 704 kilobytes • Shafuka (pages): 24 pages (main contents 16 pages)  ABUBUWAN DA YA KUNSA 1. Sujjadar Rafkanuwa   2. Nau’o’i sujjadar rafkanuwa        3. Dalilan sujjadar rafkanuwa        4. Siffofin sujjadar rafkanuwa               5. Rafkanuwar…

    Read more: Littafin Ƙabli da Ba’adi
  •  Mutuwar Sarauniyya (Queen Elizabeth II)

    Ni kam abun nan yana ɓata min rai, muna rayuwa kamar ɓangarori biyu, masu son kufular da juna. Wani lokacin, jira muke wata waƙi’a ta faru, don mu tunzura sashe. Wani lokacin kuma, jira muke, wani sashe ya yi saɓanin fahimtarmu, mu samu abun suka. Mutuwar Sarauniyya ta wuce wannan cecekucen da ake a social…

    Read more:  Mutuwar Sarauniyya (Queen Elizabeth II)
  • Kai Ne A Media, Kai Ne A Zahiri

    Kai! Kada ka yaudari kanka, kana shaƙiyanci, ƙirƙirar labaran ƙarya, batsa da sunan barkwanci ko raha a ‘media’, ka ce ai a zahiri ba haka kake ba. Da ƙarya da batsar zahiri da ta media, duk ɗaya ce.Social media is a channel of self-expression. Akwai ‘personality theories’ da yawa da ake (iya) karanta mutum. Misali,…

    Read more: Kai Ne A Media, Kai Ne A Zahiri
  • Elite vs. Influencer

    A nazarce, ba wata kalma ELITE a social media, sai dai INFLUENCER. ——————————* Shiga 👉👉 https://bit.ly/ElitedaInfluencer domin karanta cikakken rubutu game da SOCIAL MEDIA INFLUENCER—————————— Influencer shi ne mutum mai tarin mabiya a social media (followers), influencer ya karkasu zuwa yawan followers: mega (1m+), macro (40k – 1m), micro (1k – 40k), nano (mai followers kasa da…

    Read more: Elite vs. Influencer

Fasahar Zamani

Blogger

BLOGGER

* Akwai screenshots a comment section

Blogger shi ne mutumin da yake rubuce-rubuce a kan al’amuran yau da kullum da suka shafi rayuwa a shafukan yanar gizo. Za ka iya zama cikekken ‘blogger’ idan ka mallaki website, ko blogsite a Google Blogspot da Wordpress da sauransu, ta manhajojinsu ko kuma shafukansu.

• GOOGLE BLOSPOT
Wesbsite: blogspot.com
Android App: bit.ly/3IPObaQ
iSO (Apple): bit.ly/3IPOzGk (unavailable/an cire shi)

• WORD PRESS
Website: wordpress.com
Android: bit.ly/3cjsrb7
iSO (Apple): apple.co/3REi41F

AMFANIN BLOG

1. Neman kudi
Idan ka buɗe shafi a Google Blogspot.com kana iya samun kamar 300 visitors a kowacce rana, yawan samun waɗannan traffic zai baka damar ɗora tallace-tallace (ads) za su (iya) biyan ka miliyoyin kuɗaɗe a duk watan duniya.

2. Wallafa (Publishing)
A matsayin FREELANCER, za ka iya amfani da blogsite, domin wallafa rubutunka, ba tare da kana biyan so sisi ba.

3. Tallace-tallace
Ana iya tallata kaya ta blogsites kyauta, kamar a website.

MATAKIN BUƊE BLOG PLATFORM(S)

• GOOGLE BLOGPOT

1. Ka mallaki email
Idan da Blogspot za ka yi amfani wajen buɗe blogsite, da GMAIL kaɗai ake amfani.

2. Ka buɗe ‘app’ (Blogger) ko shafin blogspot.com.

3. Sai ka sa GMAIL naka wajen SIGN-IN.

4. A shafin farko na Blogspot, za ka ga CREAT YOUR BLOG, sai ka shiga.

5. sai ka saka PAGE TITLE (misali SAMPLE USER), sai ka yi NEXT.

6. Za ka zaɓi URL (sunan shafi), misali ‘usersampling.blogspot.com’ [idan akwai mai irin wannan URL din, za su ce ma, “SORRY, THIS BLOG ADDRESS IS UNAVAILABLE” ko “INVALID OR NOT SUPPORT” (idan ka yi amfani da wasu symbol, ko Kalmar da bata dace ba)], sai ka NEXT.

Shikenan, ka mallaki shafin blog da Google Blogspot.

• WORDSPRESS

1. Ka yi amfani da email.
Idan kuma da Wordpress ne, za ka iya amfani da kowanne irin ‘email account’ (Gmail, Yahoo Mail, Hotmail…).

2. Ka buɗe ‘app’ (Wordpress) ko shafin wordpress.com.

3. Idan ta website ne (wordpress.com), ka shiga GET STARTED ko START YOUR WEBSITE. Sai ka sa EMAIL, USERNAME da PASSWORD, za su tura ma CONFIRMATION ta EMAIL.

Idan ta ‘app’ ne, za ka shiga LOGIN OR SIGN UP WITH WORDPRESS. Sai ka sa EMAIL, ka danna CONTINUE. za su tura ma CONFIRMATION ta EMAIL.

4. Ka bu ɗe EMAIL, ka bu ɗe saƙon WORDPRESS ta inbox, sai ka pressing kan SIGN UP.

5. Idan a ‘app ne’ za zaɓi topic (misali, Food, Lifestyle, News, Personal, Photography…), ko kuma ka yi SKIP.

6. Za ka zaɓi THEME, sai ka CHOOSE.

7. Za ka zaɓi sunan DOMAI, misali, digitalusersample.wordpress.com.

8. Za su buɗe ma shafi YOUR SITE HAS BEEN CREATE, sai ka pressing OK

WALLAFA A BLOGSITE
Hanya mafi sauƙi ta yin publishing a BLOGSITES it ace, yin amfani ‘apps’ (Blogger/Wordpress) ko kuma ta computer (da browser).

Akwai sauran sites da za ka iya blogging da su kamar Wix.com, Medium.com, Weebly.com da sauransu.

✍️Aliyu M. Ahmad
17th Dhul-Hijjah, 1443AH
16th July, 2022CE

#AliyuMAhmad #FasaharZamani #Blog #Blogger #Wordpress

Rayuwa da Nazari

Design a site like this with WordPress.com
Get started