Category: Rayuwa da Nazari

  •  Mutuwar Sarauniyya (Queen Elizabeth II)

    Ni kam abun nan yana ɓata min rai, muna rayuwa kamar ɓangarori biyu, masu son kufular da juna. Wani lokacin, jira muke wata waƙi’a ta faru, don mu tunzura sashe. Wani lokacin kuma, jira muke, wani sashe ya yi saɓanin fahimtarmu, mu samu abun suka. Mutuwar Sarauniyya ta wuce wannan cecekucen da ake a social…

    Read more:  Mutuwar Sarauniyya (Queen Elizabeth II)
  • Elite vs. Influencer

    A nazarce, ba wata kalma ELITE a social media, sai dai INFLUENCER. ——————————* Shiga 👉👉 https://bit.ly/ElitedaInfluencer domin karanta cikakken rubutu game da SOCIAL MEDIA INFLUENCER—————————— Influencer shi ne mutum mai tarin mabiya a social media (followers), influencer ya karkasu zuwa yawan followers: mega (1m+), macro (40k – 1m), micro (1k – 40k), nano (mai followers kasa da…

    Read more: Elite vs. Influencer
  • Taimakawa Maɓarnaci a Media

    Don Allah mu fahimta ⚠️Idan mutum 1 yana taɓara, ka kawo sunansa ‘media’, promotion ɗinsa kake (ka sani, ko ba ka sani ba), ba nasiha kake masa ba, don ba ma lalle saƙonka ya isa gare shi ba. Idan yana da media handle, misali, Reels, Tiktok ko Youtube, a lokacin ‘followers/subscribers’ da watching time nasa…

    Read more: Taimakawa Maɓarnaci a Media
  • Farin Jini

    Farin jini jarrabawa ne, ba kamar yadda wasu iyayenmu mata ke ɗauka goshi ga ‘ya’yansu ba, har ya zama abin fariya a cikin ƙawaye. A gidan mai kishiyoyi, har habaici-habaici ake yi, da gore-gore ga wacce ƴarta ba ta da farin jini, har wasu suna neman maganin farin jini ido rufe, a wajen bokaye.  Wasu…

    Read more: Farin Jini
  • Dabi’a A Hira

    A Dabi’a (2) Wardaugh Ronald (2002) cikin ‘Sociolinguistics’ ya kawo nazari kan ɗabi’un mata da maza wajen magana da hirar yau da kullum na Coates (1986): Idan ‘yan uwa nisa’u (mata) na hira a tsakaninsu, yawancin abin da suke tattaunawa, abu ne da ya shafi rayuwar mu’amalarsu ta soyayya ko zaman aure, a karan kansu,…

    Read more: Dabi’a A Hira
  • Aikin Gwamnati

    Ɗaya daga cikin abin da ya kamata al’ummarmu su sauya tunani a kai; raba tsakanin AIKI da SANA’A (DOGARO DA KAI), kalmomi ne, amma suna da tasiri a rayuwarmu ta yau da kullum. A wajen mutane da yawa, AIKI, shi ne aiki mai albashi (salary) a ma’aikatar gwamnati, ko private sectors, kamar banki, kamfani ko…

    Read more: Aikin Gwamnati
  • Digiri

    Ilimi kalmar Larabci ce (العلم) dake nufin ‘sani’ ko ‘episteme’, sanin haƙiƙanin abu, ɗabi’arsa da kuma alaƙarsa da rayuwa daga “al-‘aql al-hayulani” zuwa “al-‘aql al-fa‘il” (Ibn Sinah cikin دانشنامه علایی). Ilimi shi ne kishiyar jahilci (rashin sani). Ilimi shi ne abin da ke bambanta ɗan Adam da dabba, shi ne kyautar da Ubangiji Ya bawa…

    Read more: Digiri
  • Rangwame

    #Rangwame Tabbas! An ce Gwamnatin Nijeriya za ta ƙara kuɗin data da kuɗin ƙiran waya (bit.ly/3p3lWMv). Yanzu abin da ya kamace mu shi ne neman hanyoyin samawa kanmu sauƙi da rangwame, tunda amfani da data da kuma ƙiran waya suna daga cikin ‘necessities’ na tafikar da rayuwar yau da kullum, musamma a kasuwancinmu. Ban san…

    Read more: Rangwame
  • Ka Bawa Gmail Tsaro

    𝗚𝗺𝗮𝗶𝗹 a 𝘄𝗮𝘆𝗮𝗿 𝗔𝗻𝗱𝗿𝗼𝗶𝗱 tamkar wata ƙofa ce ta shiga kowacce kafa da kake amfani da ita haɗe da Gmail naka. Na sha gargaɗar mu kan, mu kiyayi bawa mutane Gmail ɗinmu barkatai, komai kusancinmu da su.Idan mutum na iya shiga (𝗹𝗼𝗴𝗶𝗻) na Gmail naka, tamkar ka ba shi mukulli buɗe mu’amalarka da kafar sadarwa…

    Read more: Ka Bawa Gmail Tsaro
  • Mace Tagari Ta Yi Tsada

    Ba a samun mace tagari A YAU, sai da abin siyan gari (kuɗi). Idan baka da kuɗi, kana ji kana gani wanda ba kalarta ba, bai cancanci auranta ba, zai aure ta, saboda yana da kuɗin ɗaukar ɗawainiyyarta. A nazarce! Abu ne mai wuya al’umma ta sausata tsada cikin sha’anin aure. Idan kuwa haka ne,…

    Read more: Mace Tagari Ta Yi Tsada

Design a site like this with WordPress.com
Get started